Afrika ta Kudu ta fi Nigeria ƙarfin tattalin arziki

Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption Tun a watanni uku na farkon wannan shekarar ne yanayin ya fara ƙamari a ƙasashen biyu

Ƙasar Afrika ta Kudu ta sake zama ƙasar da tattalin arzikinta ya fi ƙarfi a nahiyar Afrika ciki har da Najeriya.

A shekaru biyu da suka gabata ne Najeriya ta yi ikirarin kasancewa ta farko a nahiyar, sai dai wani lissafin da aka yi kan musayar kuɗaɗen shiga ya nuna cewa Afrika ta Kudu ta zarta Najeriya wajen ƙarfin tattalin arziki.

Hukumar bayar da lamuni ta duniya, IMF ta yi amfani da alkaluman da take da su na ƙarfin tattalin arzikin kasashen biyu a bara.

Haka kuma a wannan shekarar kudin Afrika ta Kudu rand ya yi hannun riga da naira na Najeriya wajen musayarsu da dalar Amurka.

Rand ya samu tagomashin kashi 16 cikin dari, yayin da darajar naira ta fadi da kashi uku bisa hudu tun bayan da gwamnatin Najeriya ta fara tsarin kasuwa ta yi halinta wajen musayar kudaden waje da na ƙasar.

IMF ta ce tattalin arzikin Afrika ta Kudu da ya kai dala $301 biliyan ya zarta na Najeriya ne da dala biliyan biyar kawai.

Sai dai hukumar ta yi gargadin cewa duka tattalin arzikin ƙasashen biyu na fuskantar barazanar durƙushewa.