Bama-bamai sun sake tashi a Thailand

Harin da aka kai Thailand Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin.

Wasu bama-bamai sun sake fashewa a kudancin kasar Thailand, inda akallah mace guda ta rasu a jiya Alhamis.

An sake kai hari wurin shakatawa na Hua Hin a karo na biyu cikin sa'o'i 24, wasu karin bama-baman sun tashi a wurin yawon bude ido na tsuburin Phuket, da garuruwan Surat Thani da Trang.

Akallah mutane 3 ne aka tabbatar da mutuwarsu, wasu fiye da 20 suka jikkata a hare-haren da aka kai.

Shugaban sojin Thailand mai mulkin kasar Prayut Chan-O-Cha, ya yi Allawadai da kai harin.

Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai wannan hariu, sai dai wakilin BBC a birnin Bangkok yace za a zargi wata kungiyar 'yan tawaye ko masu adawa da gwamnatin sojin kasar.

Labarai masu alaka