Amurka ta samar da kudin yaki da Zika

Jariri mai cutar Zika Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Tallafin dai zai bai wa masu bincike damar gudanar da ayyukan su.

Gwamnatin Amurka ta samar da kudi dala miliyan tamanin da daya, da nufin tallafawa masu binciken samar da riga kafin cutar Zika.

Sakatariyar hukumar lafiya Sylvia Burwell ita ce ta sanar da hakan ga shugabar marasa rinjaye ta majalisar Dokokin Amurka Nanct Pelosi.

Wasikar dai ta kunshi bayanan karfafawa masu bincike gwiwar su ci gaba da gudanar da ayyukansu, duk kuwa da turjiyar da aka samu daga 'yan majalisar na gazawa wajen samar da kudaden.

A watan Fabrairun da ya gabata ne gwamnatin shugaba Obama ta bukaci majalisar dokokin kasar ta samar da dala biliyan daya da miliyan dari tara dan magance cutar Zika, amma kuma suka tafi hutu ba tare da an cimma matsaya ba.

Cutar zika da wani nau'in sauro ke yada ta, ta na yiwa jarirai illa ta hanyar haifar su da dan karamin kai da tawaya a kwakwalwar su.