Na ƙalubalanci Trump da ya bayyana harajinsa — Clinton

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hillary Clinton tare da mataimakinta, Tim Kaine

'Yar takarar neman shugabancin Amurka a karkashin jam'iyyar Democrat, Hillary Clinton ta bayyana yawan harajin da ta ke biya a shekara, a inda kuma ta nemi Donald Trump da shi ma ya yi hakan.

Bisa bayanan, Clinton ta biya haraji na kaso 34.2 ga gwamnatin tarayya, a shekarar da ta gabata.

Shi ma abokin takararta, Tim Kaine tare da matarsa, Anne Holton, sun biya haraji na kaso 20.3.

To amma dan takarar jam'iyyar Republican, Donald Trump wanda biloniya ne har yanzu yaki yarda ya bayyana abin da yake biya a matsayin haraji.

'Yan takara dai na sakin bayanai kan harajin da suke biya da irin taimakawa jam'a da suke yi ga 'yan jarida domin masu zabe su gane inda suka sanya gaba.

Shi dai mista Trump ya ce ba zai bayyana harajin da yake biya ba, har sai Hukumar Tattara Harajin cikin Gidan Amurka ta kammala bincike a kai.