Olympic: 'Yan kwallon Najeriya na yajin aiki

Image caption Siasia ya jinjina wa 'yan wasan

Tawagar 'yan kwallon Najeriya ta 'yan kasa da shekaru 23 da ke fafatawa a gasar Olympics a Brazil ta ki fita atisayi saboda ba a biya su alawus ba.

Ana sa ran bayan atisayen za su fafata da tawagar Denmark a matakin dab da na kusa da na karshe, sai dai 'yan wasan sun ce ba za su yi atisaye ba sai hukumar kwallon kafar kasar, NFF da hukumar da ke kula da gasar Olympics ta Najeriya sun biya su kudaden da suke bin gwamnati.

A wata hira da kocin tawagar Samson Siasia ya yi da gidan rediyon Brila da ke Najeriya, ya ce "komai ya hargitse saboda 'yan wasan ba sa son yin atisaye. Muna tare da su yanzu haka, kuma za mu yi dukkan abin da suke so. Mun yi daidai da suke neman hakkinsu"

Siasia ya kara da cewa shi kansa da mataimakansa sun kwashe wata biyar ba a ba su albashinsu ba, yana mai cewa hakan bai dace ba.

Labarai masu alaka