An hana sanya kayan ninkaya mai rufe jiki a Faransa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Birnin Cannes ya yi fice wajen yawon bude ido saboda yana bakin teku

Magajin garin Cannes da ke kudancin Faransa ya hana sanya kayan ninƙaya da ke rufe jiki saboda dalilai na tsaro.

David Lisnard ya ce kayan na nuni da 'tsattsauran ra'ayin Islama' ne kuma zai iya janyo faɗa, ganin yadda masu fafutukar Islama ke kai hare-hare a ƙasar.

Faransa ta shiga yanayin ko ta kwana tun bayan hare-haren da aka kai wa ƙasar, na baya-bayan nan shi ne na babbar mota a Nice.

Duk wadda aka kama da laifin keta dokar zai fuskanti tara ta $33 ko euro 38.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da ƙasar ta kafa dokar da ta shafi sanya sutura ta mata ba, a shekarar 2011 Faransa ta haramta sanya burƙa da niƙab wanda mata Musulmi ke sanya su rufe fuskarsu da su.

Labarai masu alaka