Gobarar motar mai ta kashe mutum 17 a Niger

Hakkin mallakar hoto Pankaj Raut

Kimanin mutum 17 ne suka rasa rayukansu a wata gobarar da ta tashi a motar daukar mai a kauyen Tsauni da ke jihar Damagaran a Jamhuriyar Nijar.

Sai dai an samu bayanai masu karo da juna a kan sanadin gobarar, inda wasu mazauna yankin suka ce jami'an kwastam ne suka bude wa motar wuta.

Yayin da magajin garin yankin, wanda ya tabbatar wa da BBC aukuwar hatsarin ya ce ba zai iya tabbatar da cewa harbin motar aka yi ba.

Motar dai mai dauke da jarkokin man fetur kimanin 50 ta saki hanya kana ta daki wasu shaguna uku da ke gefen hanya, inda mutane suka fake wa ruwan sama.

Cikin wadanda lamarin na yammacin ranar Alhamis ya rutsa da su har da mace guda da yara kanana.

Jihar Damagaran na fama da matsalar kisan mutane da motocin daukar mai ke yi.

Labarai masu alaka