Nigeria ta talauce — Buhari

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Darajar naira na ci gaba da faduwa

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya ce farat-daya kasar ta talauce.

Ya yi wannan kalami ne bayan wasu rahotanni sun nuna cewa Afirka ta Kudu ta sake zama kasar da ta fi karfin tattalin arziki a Afirka, shekara biyu bayan Najeriya ta yi ikirarin zama ta farko.

Shugaba Buhari, wanda ya yi wannan kalami a Abuja, ya kara da cewa, "Shekarar nan ta zo wa Najeriya cikin mawuyacin hali. Kafin mu karbi mulki ana sayar da gangar danyen man fetur a kan $100 (£77), amma da hawan mu sai ya koma $37, kuma yanzu haka ana sayar da shi daga $40 zuwa $45".

"Farat-daya mun koma kasar da ta tsiyace, amma kokarin da ake yi na tsantseni da tabbatar da gaskiya shi ke sa mutane ba sa fahimtar ainihin halin da ake ciki", in ji Shugaban na Najeriya.

Shugaba Buhari dai ya karbi mulki ne a lokacin da 'yan kasar ke matukar bukatar sauyi sakamakon matsanancin halin da suke ciki, sai dai da alama al'amura ba za su canza ciki sauri kamar yadda suka yi zato ba.

Shugaban kasar ya zargi tsohuwar gwamnatin Goodluck Jonathan da sace makudan kudade da cin hanci da rashawa, lamarin da ya sa aka kama manyan tsofaffin jami'an tsaro da 'yan siyasa wadanda ake zargi da hannu a badakalar.

Labarai masu alaka