Putin ya kori shugaban ma'aikatansa

Hakkin mallakar hoto AP

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya kori shugaban ma'aikatan fadarsa, Sergei Ivanov, daga mukaminsa.

Sergei Ivanov na daya daga cikin manyan makusantan shugaban kasar ta Rasha.

A wani mataki da ya bai wa kowa mamaki, Mista Putin ya mayar da Sergei Ivanov matsayin mai ba shi shawara kan harkokin da suka shafi muhalli.

An ambato shugaban na Rasha yana cewa Sergei Ivanov ne da kansa ya bukaci a sauke shi daga mukamin, sai dai wakilin BBC ya ce 'yan kasar Rasha ba su yarda da wannan bayani na Putin ba musamman ganin cewa zaben majalisar dokoki na gabatowa.

Mutanen biyu sun dade suna abota tun zamanin tsohuwar tarayyar Soviet lokacin da dukkansu suka yi aiki da hukumar leken asirin kasar.

Labarai masu alaka