Russia ta kai makamai zuwa Crimea

Hakkin mallakar hoto RUSSIAN DEFENCE MINISTRY
Image caption Makamai masu linzami kirar S-400 na iya rugurguza jirgi daga sama.

Sojin Russia sun sanar da kai wasu sabbin makamai masu linzami, zuwa yankin Crimea, a wani mataki na shiryawa hare-hare daga kasar Ukraine.

Kafafen watsa labarai na Russia sun ce a watan da ya gabata ne dai aka nemi a kai wa dakarun sojin da ke Crimea makaman kirar S-400.

Har wa yau, gwamnatin ta Russia ta sanar da yin atisaye a Crimea mako mai kamawa da manufar yin gwajin amfani da makaman ƙare dangi.

Firai Ministan Russia, Dmitry Medvedev, ya ce idan har rikicin yaƙi ci yaƙi cinyewa to Russia za ta iya yanke hulɗar jakadanci da Ukraine.

Tun dai shekarar 2014 ne Russia ta haɗe yankin Crimea zuwa cikin ƙasarta, al'amarin da bai yi wa Ukraine dadi ba kuma hakan ya sa suke ta gabza rikici.

Labarai masu alaka