Sudan ta kudu na adawa da dakarun MDD

Hakkin mallakar hoto AFP

Kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya amince da tura karin sojojin wanzar da zaman lafiya su 4000 zuwa Sudan ta kudu da nufin inganta tsaro a kasar.

Wani fadan da aka kwashe kwanaki ana gwabzawa a watan jiya ya yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da jefa al'umar kasar cikin mawuyacin hali.

Sai dai gwamnatin Sudan ta kudu ta yi watsi da kudurin majalisar dinkin duniyar, tana cewa abin takaici ne.

A wajen taron kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniyar, an yi ta jaddada cewa hakkin gwamnatin Sudan ta kudu ne ta kare rayukan al'umominta farar-hula.

Sai dai ana zargin sojojin kasar da hannu dumu-dumu a kisan da aka yi wa farar-hula a wani rikicin baya-bayan nan da ya barke a kasar.

Ana dai ci gaba da zaman dardar a kasar, lamarin da ya sa majalisar dinkin duniya yanke shawarar tura karin dakarunta kasar Sudan ta kudun.

An kuma fadada hurumin dakarun majalisar dinkin duniyar a wannan karon fiye da na dakarunta da aka fara turawa kasar, dangane da aikin da za su yi a Juba, babban birnin kasar, kasancewar su za dankawa aikin kare filin jirgin saman birnin da wasu muhimman gine-ginen gwamnati da sauran cibiyoyi.

Kazalika za a ba su ikon far ma duk wani bangaren sojojin Sudan ta kudun da ya kai hari kan farar-hula, ko sansanonin majalisar dinkin duniyar ko kuma masu aikin agaji.

Sai dai abin ke daure-kai shi ne yanda wadannan Sojoji za su sa kafa su taka kasar Sudan ta kudu ba tare da amincewar gwamnatin kasar ba.

Ita dai gwamnatin Sudan ta kudu na adawa da matakin majalisar dinkin duniyar na tura sojoji cikin kasarta ne, saboda a cewarta yunkuri ne na keta mata rigar-mutunci a matsayinta na kasa mai cikakken 'yanci.

Amma kwamitin tsaron majalisar dinkin duniyar, a nasa bangaren ya yi barazanar cewa zai kakaba wa Sudun ta kudu takunkumin sayen makamai idan ba ta ba da hadin kai ba.