Sojoji sun karbo birnin Manbijna Syria

Birnin Manbij Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sojoji sun kubutar da fararen hula dari biyu da 'yan IS sukai garkuwa da su a birnin.

Sojojin Syria da Amurka ke marawa baya sun ce sun karbe cikakken iko da birnin Manbij da ke iyakar kasar da Turkiyya.

Kawancen Kurdawan sun ce sun fatattaki rafoyawar mayakan IS da daga birnin, wanda ta nan ne IS ke samun kayan bukatun su.

Maimagana yawun sojojin yace ana ci gaba da gudanar da ayyukan su tabbatar da babu kowa a cikin sa, ya yin da suka kubutar da sama da fararen hula dari biyu da 'yan IS sukai garkuwa da su.

Sai dai ya ce mayakan sun gudu da kusan adadin fararen hular da aka 'yan ta, wadanda su ke amfani da su a matsayin garkuwa.

Tun a karshen watan Mayu ne dai ake fafatawa dan karbe iko da Manbij, kuma jiragen yakin Amurka sun yi ta luguden wuta ta sama dan taimakawa Kurdawa kwace birnin.

Labarai masu alaka