Cutar Zika ta bulla a Puerto Rico

Uwa da jaririn ta mai cutar Zika Hakkin mallakar hoto Flavio Former
Image caption Cutar Zika na janyo tawaya a kwakwalwar jarirai.

Gwamnatin amurka ta ayyana dokar ta baci tsuburin Puerto Rico da ke yankin karebiya, bayan samun rahotan bullar cutar Zika.

Gwamnan yankin da ke wani bangare na Amurka Alejandro Garcia Padilla shi ne ya dauki wannan mataki.

A jiya Alhamis shugaban likitocin Tuyata na Amurka ya ce ya na san kashi 50 cikin 100 na Puerto Rico za su kamu da cutar ta Zika kafin karshen shekarar nan.

Saboda an samu sama da mutane dubu goma da shuka kamu da cutar Zikar a tsuburin, ciki har da sama da mata dubu daya masu juna biyu da suka kamu da cutar.

A shekaran jiya Alhamis ne gwamnatin Amurka ta samar da kudin tallafi na dala miliyan tamanin dan taimakawa kwararru masu bincike wajen samar da allurar riga-kafin cutar, duk da cewa har yanzu 'yan majalisa ba su amince da bada kudin tallafi da gwamnati ta bukata dala bliyan daya da miliyan dari tara, tun a watan Fabrairun bana dan yakar cutar Zika.