Olympic: Najeriya ta ci Denmark 2-0

Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Nigeria 'yan ƙasa da shekara 23 ta ci ƙasar Denmark da ci 2 da nema.

Yanzu dai a wasannin Olympic a birnin Rio na kasar Brazil, Nigeria za ta kara a wasa na kusa da na ƙarshe.

Za a kara a wannan mataki ne tsakanin Nigeriyar da Jamus.

Kyaftin din Najeriya, Mikel John Obi, shi ne ya fara zura ƙwallon a ragar 'yan Denmark a zagayen farko.

Bayan hakan, Aminu Umar shi ne ya zura ƙwallo ta biyu a cikin ragar ta 'yan Denmark.

Labarai masu alaka