Sweden: Minista ta yi nadamar shan barasa

Hakkin mallakar hoto Reuters

Ministar ilmi mai zurfi ta kasar Sweden Aida Hadzialic, ta ce ta yi nadamar sahan barasa a yayin da take tuki.

Ta ce za ta yi murabus daga kan mukaminta, bayan da aka kama ta tana tukin cikin maye.

A wani jawabi mai sosa rai, Ms Hadzialic wacce ita ce minista mafi kankantar shekaru da aka taba samu a kasar Sweden ta ce kuskure mafi girma da ta taba yi a rayuwarta.

'Yansanda ne suka dakatar da Ms Hadzialic a birnin Malmo dake kudancin kasar suka bincike ta.

Na'urar gwajin shan barasar da aka yi mata ya nuna cewa adadin barasar da ta sha ya haura fiye da kima.

Ta ce ta kwankwadi kofunan barasar biyu ne.

Kasar Sweden din dai ta tsaurara dokar yin tuki cikin maye da kuma kayyade shan barasar.

Ms Hadzialic musulma ce 'yar asalin Bosnia Herzagovina da tun tana karama iyayenta suka zo da ita gudun hijira kasar Sweden.

Labarai masu alaka