IS: An ci gaba da shan taba da aske gemu

Hakkin mallakar hoto

Mazauna birnin Manbij dake arewacin kasar Syria na ta bukukuwan samun 'yanci bayan da aka kwato garin daga hannun mayakan IS.

Sun fantsama kan titina suna ta annashuwa da dabdala saboda damar da suka ce an tauye musu har na tsawon shekaru biyu.

Hakan kuwa sun hada da aske gemu da kuma shan taba sigari.

Wasu mata sun rika cire nikabin su suna konawa.

Mayakan Kurdawa dake samun goyon bayan Amurka da mayakan larabawa, sun fafata har na tsawon kwanaki 73 kafin su fatattki mayakan na IS daga Manbij dake kusa da kan iyakar kasar Turkiyya.

Fararen hula dubu biyu ne aka kubutar daga garkuwar da mayakan na IS suka dade suna yi da su.

Labarai masu alaka