Juyin mulki: An kori mutane dubu 82 a Turkiyya.

Firai ministan Turkiyya Binali Yildrim Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Firai ministan Turkiyya Binali Yildrim

Ma'aikata dubu biyar ne aka sallama, tare da dakatar da dubu saba'in da bakwai a Turkiyya, sakamakon juyin mulkin watan jiya da bai samu nasara ba.

Firai ministan Turkiyya Binali Yildirim ya shaidawa manema labarai a birnin Ankara cewa a cikin wadanda aka sallama, mutane fiye da dubu uku jami'an soji ne.

Ya ce ana zargin su ne da alaka da malamin nan mai adawa da gwamnatin kasar Fethullah Gulen,da ake zargi da kitsa juyin mulkin da bai samu nasara ba.

Ya kuma yi kira da Amurka ta taso keyar Mr Gulen zuwa gida Turkiyya don ya fuskanci hukunci.

Malamin wanda tsohon aminin shugaba Recep Tayyip Erdogan ne, na neman mafaka a jihar Pennsylvania ta Amurka.

Sai dai ya musanta zargin da ake yi masa da hannnu a yunkurin juyin mulki na farko tun a shekara ta 1997, da ya haddasa mutuwar mutane 270.

Labarai masu alaka