An fara sanar da sakamakon zaben Zambia

Image caption Masu zabe a Zambia

Sakamakon farko-farko na zaben shugaban kasa a Zambia na nuna shugaban mai ci, Edgar Lungu ne ke kan gaba.

An sanar da sakamakon mazabu fiye da ashirin daga cikin dari da hamsin da shida, kuma ana sa rai a sanar da sakamakon karshe a ranar Lahadi.

Tun da farko, hukumar zaben kasar ta yi watsi da zargin da dan takara na bangaren adawa, Haikainde Hichilema ya yi, cewa ta hada baki da jam'iyya mai mulki don a jinkirta sanar da sakamakon zaben.

A bara ne aka zabi shugaba Edgar Lungu da kankanin rinjaye, bayan rasuwar shugaban kasar na wancan lokaci Michael Sata.

Labarai masu alaka