Chibok: Mahaifi ya gane 'yarsa a bidiyo

Hakkin mallakar hoto Boko Haram

A Najeriya, daya daga cikin iyayen 'yan matan Chibok da kungiyar Boko Haram ta sace a shekarar2014 ya ce ya gane 'yarsa a sabon bidiyon da kungiyar ta fitar.

Mista Samuel ya shaida wa BBC cewa hankalinsa ya tashi sosai da ya ga 'yarsa, Serah Samuel tare da sauran 'yan matan, inda suke mika bukatar gwamnati ta sa baki a sako su.

Ya ce ganin 'yar tasa da rai ya kara masa kwarin gwiwar cewa wata rana za su sake haduwa.

Mista Samuel ya ce shi da wasu iyayen 'yan matan sun fara tattaunawa, kuma wani nauyi ne akansu na ganin sun gana da shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, kamar yadda yaran nasu suka bukace su da yi.

Ya ce duk da cewa wasu daga cikin 'yan matan sun mutu, suna bukatar a ceto musu wadanda suke raye, koma a cikin wane hali suke.

Sai dai ya ce har yanzu, ba su ga irin kokarin da gwamnatin Najeriyar ke cewa tana yi ba game da ceto 'yan matan na Chibok.

Labarai masu alaka