Chibok: "Sabon bidiyo zai zama sila na ceto"

Hakkin mallakar hoto Lai Mohammed Facebook
Image caption Ministan watsa labarai na Najeria, Lai Mohammed

Gwamnatin Najeriya ta ce tana daukar dukkan matakan da suka dace wajen ganin an ceto 'yan matan Chibok tare da kawo karshen rashin kwanciyar hankali sakamakon sace su da aka yi.

Ministan watsa labarai na kasar, Alhaji Lai Mohammed, ya sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa, yayin da yake mayar da martani ga sabon bidiyon Boko Haram ta fitar.

"Muna bakin kokarinmu a kan lamarin. Amma dole ne muyi taka-tsantsan saboda yadda lamarin ya kara cukurkudewa sakamakon rabuwar kai da aka samu a shugabancin kungiyar Boko Haram", Inji Lai Mohammed.

Haka kuma ministan ya ce suna kara yin taka-tsantsan domin kare lafiyar 'yan matan.

Ya kara da cewa "tun da wannan ba shi ne karo na farko ba da ake tuntubar mu a kan wannan lamari, muna so mu samu tabbacin cewa mutanen da muke magana da su, su ne na hakika ni".

Alhaji Lai Mohammed ya yi fatan cewa wannan bidiyo da aka fitar yanzu, zai zama mafarin kawo karshen kunci da 'yan matan da iyayensu da kuma dukkan 'yan Najeriya suke fama da shi game da sace 'yan matan.

Wannan ne karo na uku da kungiyar Boko Haram ke fitar da bidiyon 'yan matan na Chibok da ta sace a shekarar 2014.

Labarai masu alaka