Nijar: Jam'iyyar adawa za ta shiga gwamnati

Hakkin mallakar hoto

A jamhuriyar Nijar jam'iyar MNSD Nasara mai adawa, ta amince ta shiga gwamnatin hadin kan kasa da shugaban kasar Alhaji Mahamadou Issoufou ya yi wa 'yan adawar tayi a jawabinsa na ranar 2 ga wannan watan.

Jam'iyar MNSD Nasara ta dau wannan matakin ne bayan wani taro da kwamitin kolinta ya yi jiya, har tsakiyar daren da ya gabata.

Daga cikin mambobi 203 da kwamitin kolin ya kunsa 148 ne suka halarci taron inda 144 suka amince da matakin.

Babban sakataren jam'iyar, Alhaji Tijani Abdulkadri ya ce ba dan mukami zasu shiga gwamnati ba, sai don ganin halin da kasar take ciki.

Kuma ya ce, sun shiga gwamnati ne don yiwa talakawan kasa aiki.