An kaddamar da banki mara amfani da kudi a Nigeria

A karon farko a tarihin Nigeria, an kaddamar da wani banki wanda ba ya amfani da takardun kudi a jihar legas.

Hamshakin dan kasuwar nan wanda ya fi kowa arziki a nahiyar Afrika, Aliko Dangote ne ya bayar da shawarar kafa bankin na Sun Trust.

Tsarin na sabon bankin dai kwata-kwata baya amfani da takardun kudi kamar yadda aka sani a sauran bankuna.

Tun a shekarar 2001 ne aka bayar da lasisin kafa bankin.

Sai dai wasu masu sharhi na ganin rashin ingantacciyar hanyar sadarwa ta intanet da karancin wutar lantarki za su iya zama manyan kalubale ga ayyukan bankin.