An kai samame a kotunan Turkiyya

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Sai dai Gulen ya musanta hannu a yukurin juyin milkin da aka yi wa shugaba Recep

'Yan sanda da ke bincike a kan yukurin juyin mulkin da aka yi a Turkiyya, sun kai samame kan wasu kotuna uku da ke birnin Istambul.

Samamen ya zo ne bayan an bayar da takardar izinin kama wasu lauyoyi masu shigar da kara da wasu ma'aikatan kotuna fiye da 170.

An bincika wasu ofisoshi kuma an tsare wadansu mutane.

Gwamnatin kasar ta dora laifi yunkurin juyin mulkin a kan wani malamin addinin musulunci, Fethullah Gulen da ke zaune a Amurka.

Ana tsare da dubban sojoji da kuma fararen hula da ake zargin da hannu a yukurin juyin mulkin, a yayin da gwamnati ke kokarin dakile kungiyar Gulen.