An ƙirƙiro manhajar sauƙaƙa aikin Hajji

Hakkin mallakar hoto AP

Domin shawo kan matsalar da mahajjata suke fuskanta a Mina da Arfa yayin aikin Hajji, wasu masu aikin sa kai 'yan Pakistan da India, sun ƙirƙiro wata manhajar wayar salula da za ta shawo kan matsalar.

Manhajar da za ta soma aiki daga ranar 7 ga watan Dhul Hajj zata sauƙaƙawa maniyyata gano masaukinsu a Makkah: da Mina, da kuma Arfa.

Jagoran aikin kirkiro manhajar Muammad Shahid Farooq ya fadawa jaridar Arab News ta Saudiyya cewa, a duk shekara alhazai da dama suna ɓata, wasu kuma su kwashe lokaci mai yawa kafin su gano hemarsu a Mina, ko su gano inda abokan tafiyarsu suke, ko kuma gano inda masaukinsu yake a Makkah.

Ya ce, manhajar zata saukaka yadda masu aikin hajji zasu gano hanyoyin da ya kamata su bi zuwa masauƙi, da tashohin jirgin kasa, da masallatai, da kuma asibitoci, da kuma saukaka zirga-zirga a Mina.

Wadanda suka kirkiro manhajar sun kuma ce, sun yi ta ne ta yadda zata iya aiki a wayar salula koda babu Internet.

Labarai masu alaka