Ban Ki-Moon na son mace ta gaje shi

Hakkin mallakar hoto AP

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya ya ce zai so mace ta gaje shi.

Ban Ki-moon ya ce lokaci ya yi na samun shugaba mace, bayan majalisar ta shafe shekaru 70 a karkashin jagorancin maza takwas.

Mata biyar ne a cikin 'yan takara 11 da ke neman shugabancin majalisar.

Kafin a zabi sabon shugaban Majalisar Dinkin Duniyar, sai kasashe 15 da ke kwamitin tsaro na majalisar da kuma sauran kasashe 193 a zauren majalisar sun nuna amincewar su da shi.

Ana sa ran za a sanar da wani sabon babban sakataren a watan Disambar bana.

A al'adance dai ana karba-karbar mukamin ne a tsakanin nahiyoyin duniya.

Labarai masu alaka