Burtaniya ta samu Choudary da laifin marawa IS baya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Anjem Choudary yana wa'azi mai zafi

An samu Anjem Choudary, daya daga cikin malaman Burtaniya masu tsaurin ra'ayin addini, da laifin jan hankalin mutane wajen goyon bayan kungiyar IS.

A 2014 ne dai aka kama Anjem Choudary, mai shekara 49, bayan da ya yi wa kungiyar ta IS mubaya'a.

'Yan sanda sun ce an samu mutane da dama da laifukan ta'addanci sakamakon wa'azin da Choudary yake yi.

An dai yanke wa Choudary hukunci ne tare da amininsa, Mohammed Mizanur Rahman.

Jami'ai masu yaki da ta'addanci sun kwashe shekaru 20 suna kokarin kai Choudary kotu kan taimakon kungiyar ta'addanci musamman sanyawa matasa maza da mata tsauraran akidu.

An dai tuhumi Anjem Choudary da Mohammed Rahman da laifin neman a goyawa IS baya, abin da ya ci karo da dokar ta'addanci ta Burtaniya.

Tun ranar 28 ga watan Yuli ne aka yankewa mutanen hukunci amma kuma sai yanzu ne kafafen yada labarai suka yada.

Labarai masu alaka