Chibok: Gida nake son komawa — Amina

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Amina Ali tare da Buhari da gwamnan Borno, Kashim Shettima

Ɗaya daga cikin 'yan matan nan na Chibok fiye da 200 da Boko Haram ta sace, wadda aka ceto ta, Amina Ali ta ce gida take son komawa.

A wata hira da kamfanin Dillancin Labarai na Reauters, a Abuja, ranar Talata, yarinyar ta ce babu abun da take so illa ita koma gaban iyayenta.

Tun dai watan Mayu gwamnatin Najeriya ke ajiye da Amina tare da jaririyarta da manufar killace ta, bayan da aka ceto ta daga hannun Boko Haram.

Amina ta ce ba ta da tabbacin ko za ta koma makaranta sannan kuma ba ta san lokacin da za ta koma garinsu ba.