Amurka ta kwashe Fursunoni 15 daga Guantanamo

Hakkin mallakar hoto McCoy Reuters
Image caption Shugaba Obama na son ya rufe sansanin kafin ya sauka daga kan mulki

Ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon, ta sanar da tura fursunoni 15 da ake tsare da su a gidan wakafi na Guantanamo Bay, zuwa Tarayyar Daular Larabawa.

Fursunonin da aka kwashe daga sansanin da ke kasar Cuba, sun hada da mutane 12 'yan kasar Yemen da kuma 'yan Afghanistan uku.

Shugaba Obama na Amurka ya yi amanna cewa kurkukun na taimakawa wajen sanya mutane shiga kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi, kuma yana janyo bakin jini ga Amurkar.

Fursunonin su ne mafi yawa da aka mika zuwa wata kasa a lokacin mulkin shugaba Obama.

An daure fursunonin da aka sake yanzu har tsawon shekara 14 ba tare da an tuhume su da aikata wani laifi ba.

Kuma kawo yanzu an kwashe furunoni 61 kenan daga sansanin na Guantanamo mallakar Amurka.

Sai dai yunkurin shugaba Obama na mayar da sauran fursunonin da suka rage zuwa Amurka ya gamu da turjiya daga majalisar dokokin kasar.