Matsalar fyade ta yi kamari a Afrika ta Kudu - MSF

Kungiyar agajin likitoci ta MSF ta wallafa wani rahoton ya bayyana cewa matsalar fyade ta yi kamari a yakin hako ma'adin Platinum a Afrika ta Kudu.

MSF ta bayyana cewa mata da yara mata 11,000 ne ake yiwa fyade duk shekara, inda a mafiya yawan lokuta abokan zamansu ne ke yi musu fyaden.

Kungiyar ta kara da cewa a kwaryar birnin Rustenberg mace daya cikin hudu na iya fuskantar fyade a rayuwarsu.

Likitocin sun kuma nuna damuwar cewa kashi biyar cikin dari ne na matan da abin ya shafa ke kai rahoto ga ma'aikatan jinya.

Yayin da kalilan ne kuma suka san abin da za su yi idan suka kamu da cutar HIV.

MSF ta nuna bukatar kafa asibitoci da cibiyoyin shan magani cikin gaggawa domin bayar da kulawa ga masu bukata.

Labarai masu alaka