Nigeria na buƙatar ƙara yawan man da take haƙowa

Hakkin mallakar hoto twitter

Karamin ministan man fetur na Najeriya Emmanuel Ibe Kachikwu ya ce kasar na bukatar ta rika fitar da gangar mai miliyan uku da dubu dari daya a kowace rana yanzu, kafin ta iya samun issassu kudaden aiwatar da kassafin kudin bana.

An dai tsara kassafin kudin ne bisa hasashen kasar za ta rika fitar da gangar danyen mai miliyan biyu da dubu 200 a kowace rana kuma za a sayar da kowace gangar kan dala 38.

Sai dai sakamakon dawowa da kai hare-hare kan bututan mai a kasar a watan Febrairu' sai yawan man da kasar ke fitarwa ya ragu zuwa ganga miliyan daya da rabi a rana.

Mista Kachikwu ya shedawa gidan talabijin na CNN cewa sakamakon hare-haren da ake kaiwa na kimannin watanni shida, Nigeria ta yi hasarar kudade masu dimbin yawa, sabo da raguwar yuwan man da take futarwa zuwa ganga miliyan daya da rabi, a maimakon ganga miliyan biyu da dubu 200.

Dan haka yanzu kasar tana bukatar futar da sama da ganga miliyan uku domin cike gibi.

To sai dai wasu masana na ganin idan gwamnati ta toshe hanyoyin da ake satar man fetur a kasar, yawan man da ake hakowa zai karu.

Labarai masu alaka