Cutar shawara ta kashe mutane 400

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption ANGOLA

Mutane 400 sun mutu sanadiyyar kamuwa da cutar shawara wato, Bayamma ko kuma farar masasara a kasashen Dimokaradiyar Kongo, da kuma Angola.

Sama da mutane dubu 6 ne suka harbu da cutar a wadannan kasashe guda biyu.

Kungiyar agaji ta Save the Children ta Birtaniya ta yi gargadi game yaduwar cutar.

Ta sanar da cewa cutar na iya bazuwa zuwa wasu bangarorin duniya kamar su Turai da Amurka da kuma Asia.

Kungiyar agajin ta Save the Children ta ce, zata soma gudanar da riga kafin cutar ga mutane rabin-milyan a Kinshasa babban birnin kasar ta Kongo.

Shi dai wannan zazabi na Yellow Fever dake hallaka bil'adama wanni irin sauro ne da ake samu a kasashen yamma ke yada cutar.

Labarai masu alaka