'Yan tawaye sun kashe mutane 7 a Saudiyya

Hakkin mallakar hoto AP

Kafofin yaɗa labaran Saudiyya sun ce, harin roka na 'yan Houthi dake tawaye a Yemen ya kashe mutane bakwai a cikin Saudiyya.

Gidan talabijin din Saudiyya, wato Ekhbariyah ya ce, rokokin da 'yan tawayen Houthi suka harba sun sauƙa a yankin masana'antu na garin Najran dake kudancin Saudiyyar.

Waɗanda suka mutu sun haɗa da 'yan Saudiyya 4, da ma'aikata 'yan ƙasashen waje 3.

Kafin nan dai mazaunan unguwar Nehm dake gabashin Sana'a babban birnin Yemen sun ce, harin dakarun haɗin gwiwa da Saudiyya ke jagoranta akan gidan daya daga cikin shugabannin 'yan Houthi ya kashe mahaifinsa da iyalansa 8.

Amma lokacin da aka kai harin shi ba ya gidan.

Labarai masu alaka