An kori garken zuma daga asibiti

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

An fatattaki kudan zuma sama da dubu dari daga wani asibiti a birnin Wales na Birtaniya, bayan wani dattijo marar lafiya ya lura da ruwan zuman na zubowa daga saman gini.

An dai kira kwararru da suka san kudan zuma, a lokacin da aka gano sakar da suka yi har a wuri biyu, a saman ginin asibiti a makon da ya wuce.

Ana ganin dai akalla kudan zuman sun kai shekaru biyar a asibitin ba tare da na san da zaman su ba, hakan ya sanya suka yi ta yaduwa har suka sake yin wata sakar.

An dai danganta gano sun da aka yi, da sauyawar yanayi na zafi wanda shi ya janyo narkewar zuman har ya fara zubowa kasa ta rufin ginin.

Masu aikin kwashe su dai sun shafe tsahon mako guda su na aikin, inda suka sama musu wani wuri kebantacce da za su ci gaba da yin saka.

Sauran abun da ya ragu daga zuman a ginin asibitin za a yi amfani da shi wajen yin Sabulun wanka, da kyandir, da kuma abin da ke sanya katako ya yi kyalli.

Labarai masu alaka