Ƙiba ta janyowa mata rasa aiki a Masar

Hakkin mallakar hoto Channel 2
Image caption Hukumomin gidajen talabijin na Masar sun ce matan sun yi kiba da yawa

Hukumomin gidan talabijin a Masar sun dakatar da mata takwas da ke gabatar da shirye-shirye a talabijin, sannan aka ce umarce su ringa motsa jiki.

Lamarin dai ya janye ce-ce ku-ce daga kungiyoyin masu fafutuakar kare haƙƙoƙin mata.

Ƙungiyar ma'aikatan gidajen radiyo da talabijin ta kasar ta Masar ta bawa matan wata guda domin su rage ƙiba, kafin su sake bayyana a akwatunan talabijin.

Ɗaya daga matan da wannan hukuncin ya shafa Khadija Khattab ta shedawa gidan jaridar Al-Yaum cewa tana so mutane su kalli shirye-shiryen ta na baya-bayannan, sannan su yanke hukunci ko ta yi ƙiba da yawa, sannan kuma su tantance ko ya kamata aiki.

Wata matar da lamarin ya shafa kuma cewa ta yi, matakin ya fusata danginta.