Barasa ta kashe mutane a India

Hakkin mallakar hoto AFP

Jami'ai a jihar Bihar da ke gabashin India suna binciken mutuwar mutane 13 bayan sun sha barasa.

An dai kwantar da mutanen ne asibiti bayan sun yi fama da ciwon ciki da kuma amai.

Iyalansu sun ce mutanen sun sha barasa ta gargajiya da aka haramta, sai dai hukumomi sun musanta haka.

A watan Afrilu, jihar ta Bihar ta kafa wata doka ta haramta saye da kuma shan barasa.

Mutane da dama sun yi maraba da dokar, musamman ma mata wadanda suke ganin shan giya na janyo tashe-tashen hankula da kuma munanan dabi'u.

Jihar na fama da talauci da matsanancin rashin aikin yi.

Labarai masu alaka