Valls ya goyi bayan hana Musulmai sa kayan ninƙaya

Firai ministan Faransa, Manuel Valls, ya fito ƙarara ya goyi bayan hana mata Musulmai sanya kayan ninƙaya mai rufe jiki a wasu sassan ƙasar.

A wata hira da wata jaridar Faransa mai suna La Provence, Mista Valls ya bayyana cewa saka kayan ninƙayan da ke rufe jiki, wata hanya ce ta ci gaba da ƙasƙantar da mata wanda bai zo daidai da al'adun Faransa ba.

Ko da yake ya ce haramcin ba zai kawo ƙarshen hare-haren ta'addancin da ƙasar ke fuskanta ba.

Birane bakwai ne da ke bakin teku a ƙasar ta Faransa suka sa dokar haramta sanya kayan ninƙayan da mata musulmai amfani da shi.

Labarai masu alaka