An haramta bikin aure da daddare a Kenya

Hukumomi a ƙasar Kenya sun haramta shagulgulan aure da daddare a yankin Mombasa da ke bakin teku, saboda dalilai na tsaro.

Kwamishinan da ke kula da yankin, Maalim Mohammed, ya ce an dauki matakin ne domin a kare mazauna yankin daga hare-haren da wasu gungun mutane ke kai wa da wuƙa a kan mutane.

A baya-bayan nan dai yankin na Mombasa na fama da matsalar gungun masu aikata laifuka, inda mazauna yankin suke kai rahoton fashi da ake musu da tsakar rana.

'Yan sanda sun sha kai farmaki yankin, inda suka suka harbe wadanda ake zargin 'yan gungun ne da dama.

Mazauna yankin na kwashe kwanaki suna shagulgulan bikin aure tare da yin liyafar dare.

Labarai masu alaka