An samu jinkirin jigilar mahajjata a Niger

A jamhuriyar Nijar an samu jinkirin jigilar mahajjata zuwa ƙasar Saudi Arabia, domin aikin hajjin bana.

A ranar Talata da daddare ne yakamata ace jirgi na farko dauke da maniyyatan zuwa Saudiya,amma hakan ba ta samu ba.

Hukumar hajji da umara ta kasar COHO ta ce matsalar ta samo tushe ne daga kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Niger Airways, wanda shi ne aka ba kwangilar jigilar maniyyatan sai dai bai samu jirgi ba.

Kimanin maniyyata 12,712 ne za su tafi aikin hajji bana daga Nijar.

Hukumar tsare-tsaren hajjin na sa ran kammala jigilar maniyyatan a ranar 31 ga watan da muke ciki.

Labarai masu alaka