'Yan sanda sun killace wajen taron PDP

Hakkin mallakar hoto pdp
Image caption Jam'iyyar ta PDP na fama da rigingimu na cikin gida

Rahotanni daga birnin Fatakwal da ke jihar Rivers a Nigeria na cewa 'yan sanda sun killace wajen da jam'iyyar adawa ta PDP ta shirya gudanar da babban taronta.

Wani jami'in jam'iyyar ya shai da wa BBC cewa an hana su shiga filin wasan kwallo na Sharks, inda aka shirya yin taron.

Haka kuma jam'iyyar ta wallafa hotunan jami'an tsaro a shafinta na Twitter, wadanda ta ce sun hana gwamnan jihar mai masaukin baƙi fita daga ofishinsa.

A ranar Talata ne wasu manyan kotuna biyu a ƙasar suka bayar da umarni masu cin karo da juna game da taron.

Sai dai wani bangare na jam'iyyar ta PDP ya sha alwashin yin taron a jihar Rivers da ke kudancin Najeriya.

Labarai masu alaka