An kashe mutane a Rasha

Hakkin mallakar hoto AP

Jami'a a Rasha sun kashe mutane hudu a binin St Petersburg yayin wani sumame da suka kaiwa wasu da ake zargin 'yan taweye ne daga gundumar Caucaus.

Jami'an rundunar yaki da ta'addanci sun ce mutanen sun bude wuta ne yayin da sojojin rasha na musamman su ka nemi su mika wuya.

Dama dai ana neman uku daga cikin su bisa dangantaka da hare haren ta'addanci da kuma yunkurin kisan kai.

An dai saba kai sumame kan masu zafin kishin addini a arewacin gundumar ta Causaus, sai dai ba a saba ganin haka a birnin St Petersburg ba, wanda shi ne birni na biyu mafi girma a Rasha bayan birnin Moscow.