Yaro ya tsallake rijiya da baya a Aleppo

Wani yaro a Aleppo Hakkin mallakar hoto
Image caption Masu mu'amala da dandalin sada zumunta sun kadu da ganin halin da yaron yake ciki

Masu fafutuka a Syria sun fitar da hoton wani yaro wanda aka ceto daga baraguzan wani gini a Aleppo bayan kai wani hari ta sama.

Bidiyo da kuma hotunan da aka fitar na yaron sun nuna shi yana zaune a cikin wata motar daukar marasa lafiya jikinsa duk jini.

Wani likita ya shaida yaron inda ya ce sunansa Omran Daqneesh, dan shekaru biyar a duniya, kuma ana kulawa da raunukan da ya samu a ka.

Ana kyautata zaton 'yan uwansa guda uku da kuma iyayensa duka sun tsira daga harin.

Fada tsakanin dakarun gwamnatin Syria, wadanda sojin Rasha ke taimakawa ta hanyar kai hare-hare ta sama, da kuma 'yan tawaye ya kara munana a baya-bayan nan.

Lamarin dai ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane.

Dubban yara ne suka rasa rayukansu a tsawon shekara biyar da aka yi ana yaki a kasar ta Syria.

Labarai masu alaka