Burtaniya: Tsanar bakar-fata ta karu

Kabilu marasa rinjaye a Birtaniya
Image caption Rahoton yace lamarin ya fi kazanta cikin shekaru biyar da suka gabata.

Wani sabon rahoto da aka fitar a Burtaniya, ya nuna cewa bakar-fata da kabilu marasa rinjaye a kasar na fuskantar mummunan rashin daidato da wariya a wasu yankuna, kuma lamarin ya kara munana cikin shekaru biyar da suka gabata.

Rahoton na hadin-gwiwa da hukumar daidaito tsakanin al'uma da hukumar kare hakkin bil'adama ta Human Rights suka fitar , ya bayyana yadda aka samu karuwar kai aikata muggan laifukan da suke nuna tsana tun bayan ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai a watan Yunin da ya wuce.

Rahoton ya yi hasashen cewa adadin bakar-fatan da ke fuskantar barazanar hallakawa da yanke musu hukuncin kisa ya rubanya da kashi uku.

Sai dai a nata bangaren, gwamnatin Birtaniya ta ce tana kokarin yin garanbawul a bangaren shari'ar kasar, kuma hakan za ta faru nan ba da jimawa ba.

Labarai masu alaka