Wutar daji ta barke a jihar California

Barnar da wutar daji ta yi wa California Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wannan shi ne karo na shida da jihar ke fuskantar wutar daji mafi muni.

Masu aikin kashe gobara sun fara samun nasarar shawo kan gobarar daji da ta tilasta wa fiye da mutane 80,000 tserewa daga muhallansu.

Sai dai masu hasashen yanayi na Amurka, sun ce wuri kadan ne aka ciyo kan matsalar a kusa da San Bernardino.

Wakilin BBC yace tilas aka rufe biyu daga cikin manyan hanyoyi jihar, wadanda wutar ta mamaye, wutar na tasowa ne daga bangaren wasu tsaunuka da ke wajen jihar saboda iska mai karfi da ake yi.

Jami'ai a yankin sun ce wutar ta lalata gidaje da kadarori masu tarin yawa, kuma wannan shi ne karo na shida da jihar California ke fuskantar gobarar daji mafi muni.

Jami'an sun kara da gargadin cewa yawancin iyalan da suka tsere za su dawo su tarar da gidajensu sun zama kufai.