Gambu 'mai waƙar ɓarayi' ya rasu

Image caption Gambo ya tuba daga wakar barayi kafin mutuwar sa da shekara bakwai

Allah ya yiwa shahararren mawakin nan na ƙasar Hausa Muhammad Gambo Fagada (Gambu mai waƙar ɓarayi) rasuwa.

Gambo ya rasu ne a ranar Laraba da daddare bayan ya sha fama da rashin lafiya, a garin Mai Yama da ke jihar Kebbi a Arewa maso Yammacin Najeriya.

Ya rasu yana da kimanin shekaru 67 a duniya.

Mawaƙin ya shahara da waƙoƙin ɓarayi, a lokacin da yake waƙa, to sai dai ya tuba da waƙoƙin na ɓarayi kimanin shekara shida da suka gabata, a yayin wani biki da aka yi a birnin Sakkwato.

Wani makusancin marigayin, kuma manazarci kan adabin Hausa, Farfesa Ibrahim Malumfashi, ya shaida wa BBC cewa mafi yawancin miyagun labaran da Gambo ke bayarwa a waƙoƙinsa ƙirƙira ce kawai irin ta mawaka.

Ya rasu yana da mata hudu da 'ya'ya da jikoki da dama.

Za a yi jana'izarsa da misalin karfe biyu na rana a ranar Alhamis.