Machar ya bar kasar Sudan ta Kudu

Tsohon mataimakin shugaban Sudan ta Kudu, Riek Machar, ya fice daga kasar 'yan makonni bayan sojojinsa sun kwabza kazamin fada da dakarun gwamnati wanda ya janyo asarar rayuka a birnin Juba.

Mai magana da yawun Mista Machar, James Gatdet Diak, ya ce ya koma wata makwabciyar kasar da zama, amma bai bayyana sunan kasar ba.

Shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kiir, ya kori mista Machar a watan Yulin da ya gabata.

A baya dai tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce ba zai koma Juba ba sai an kai wasu dakaru da basa goyon bayan kowane bangare domin su bashi kariya.