Masu aikatau a Saudi Arabia na tsaka mai wuya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dole ne duk bakin haure da ke aiki a Saudia su samu wani dan kasar ya tsaya musu

'Yan kasashen waje da ke aiki a kasar Saudi Arabia za su iya fuskantar tara da kora daga kasar da kuma haramta shiga kasar har abada, matuakar suka guje daga wanda ya dauke su aiki, ko kuma wanda ya tsaya musu kafin a duke su aiki.

Hukumar da ke kula da shige da fice ta kasar ta kuma yi kira ga yan Saudia da kada su bada aiki ga duk wanda ya gujewa wajen aikin sa.

Hukumar ta ce idan kuwa su ka basu aiki, suma za su iya fuskantar tara ko kuma dauri a gidan yari.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama sun jima suna kiraye-kirayen a kauda tsarin na cewa sai wani ya tsayawa masu neman aiki, suna masu cewa wani salo ne na bauta.

Labarai masu alaka