Dan adawa ya zama magajin garin Nelson Mandela

Hakkin mallakar hoto

An zabi wani dan adawa a matsayin magajin garin Nelson Madela Bay a Afrika ta Kudu.

Wannan ne karo na farkon da wani wanda ba dan jam'iyyar ANC ba zai rike wannan mukami a birnin tun bayan kawo karshen mulkin wariyar launin fata.

Kansiloli na jam'iyyar ANC wadanda suka sha kaye a zaben kananan hukumomin da aka yi, sun fice daga wajen zabne bayan Athol Trollip na jam'iyyar Democratic Alliance ya lashe zaben.

Nelson Mandela Bay - wanda ya hada da birnin Port Elizabeth - a nan ne mafiya yawan jagororin yaki da wariyar launin fata a lokacin mulkin tsiraru fararen fata suka zauna.

A ranar Laraba ne, biyu daga cikin manyan jam'iyyun adawa na Afrika ta Kudu suka amince su yi aiki tare domin tunkarar jam'iyyar ANC a manyan birane uku .

Labarai masu alaka