Fursuna 18000 ne suka mutu a Syria

Fursunoni  a Syria Hakkin mallakar hoto
Image caption Ana zargin gwamnatin Syria da gallazawa wadanda ake tsare da su a gidajen kaso.

Kungiyar kare hakkin bil'adam ta Amnesty international ta ce kusan mutane dubu sha takwas ne suka mutu da a kurkukun da gwamnatin Syria ke tsare da su tun daga fara yakin basasar kasar shekaru biyar da suka gabata.

Amnesty ta ce ana azabtar da mutanen da ake tsare da su, ta hanyar lakada musu duka, da sanya musus wutar lantarki a jiki, da kuma yi musu fyade.

A rahoton da kungiyar ta fitar, ta yi bayani kan wasu mutane sittin da biyar da aka azabtar da su a lokacin da suke tsare.

A kowacce rana mutane goma na rasuwa a gidajen kason Syria cikin shekaru biyar da aka kwashe ana yaki a kasar. Wanna shi ne adadin da rahoton Amnesty ya bayyana, kuma rahoton yace watakil adadin ma ya fi haka.

Wadanda Amnesty ta gana da su dai sun ce yawancin fursunonin kan mutu ne sakamakon lakada musu dukan kawo wuka da aka yi. Gwamnatin Syria dai ta sha musanta irin wannan zargin.

Labarai masu alaka