Tauraruwar Hollywood ta ba da sadakar $7m

Hakkin mallakar hoto Reuters

Tauraruwar fina-finan Hollywood, Amber Heard, za ta bayar da sadakar $ 7 miliyan na yarjejeniyar da suka cimma da mijinta, Johnny Depp na sakinta da ya yi.

Amber ta ce za a raba kuɗin ne tsakanin asibitin yara da kuma ƙungiyar masu fafutukar kare hakkin fararen hula, wadda za ta yi amfani da kuɗin wajen kawo ƙarshen cin zarafin mata.

Kudin ya kai naira biliyan biyu da rabi na Najeriya.

A al'adance a kasashen yamma, ma'aurata kan zana yarjejeniya wadda idan suka rabu wani bangare zai bayar da wani kaso na dukiyar da suka mallalaka ga daya bangaren.

'Yar wasar ta zargi mijinta, Johnny Depp -tauraron fina-finan Pirates of the Caribbean da marinta tare da jifanta da wayar salula a lokacin da suka yi fada.

Zargin da mijin nata ya musanta.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Amber da kumatunta a kurje a watan Mayu

Amber mai shekaru 30 ta auri Johnny mai shekaru 53 ne a watan Fabrairu 2015, kuma sun sanar da rabuwarsu a watan Mayun da ya gabata.

Lauyan mijin ya ikirarin cewa ta da zargi Johnny ne saboda ta samu kuɗi sosai bayan sun rabu.

A wata sanarwar da Amber ta fitar ta ce "Kudi ba su da wani tasiri a gare ni, sai dai in yi sadaka da su domin in taimaka wa marasa karfi."

Inda ta kara da cewa kudin $7 miliyan bai kai abin da ta ke bayarwa sadaka a baya ba, kuma ba wai ta daina yin sadaka ba ne da ga shi.

Taurarin biyu dai sun sanar da mutuwar auren ne a ranar Talatar da ta gabata.