Bolt ya sake cin zinare

Usain Bolt Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dan wasan ya yi nasara ne akan kasar Japan.

Dan wasan tseren Jamaica Usain Bolt ya jagoranci tawagar kasar, a tseren mutum hudu na mita dari a gasar wasannin Olympics da ake gab da kammalawa a birnin Rio na Brazil.

Usain Bolt ya samu nasarar cin zinare a tseren da suka yi, inda ya tsallake layi na karshe cikin wani sabon salo da ya bashi damar tserewa dan wasan Japan wanda ya ci azurfa.

Wannan nasara ta sanya Bolt ya samu zinare na uku a wasannin da ya yi.

Bayan kammala wasan Usain Bolt ya burge 'yan kallo da masu daukar hoto, inda ya karkacewa da irin salon daukar hoto da aka san shi da shi.

Ya kuma fadi irin farin cikin da ya ke ciki da alfahari da kan shi kan nasarar da ya yi.

A halin yanzu dai shi ke rike da kambin tseren mita dari, da na mita dari biyu na Olympics tun fiye da shekaru goma.